Connect with us

Ƙetare

Paparoma Leo ya soki Amurka da Isra’ila kan rikicin da suke da Iran

Published

on

Shugaban darikar Katolika Paparoma Pope Leo  ya yi kakkausar suka kan hare-haren soji da Amurka da Israel ke kaiwa kan Iran, inda ya bayyana cewa addini ba ya halatta yaƙi, yana mai cewa “Allah ba ya albarkaci kowanne irin rikici.”

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Paparoman ya nesanta addinin Kirista da yaƙe-yake.

 

Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke ƙaruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan jerin hare-hare da aka kai kan Iran, lamarin da ke ƙara tayar da hankali da yaƙi a yankin na gabas ta tsakiya.

Paparoman ya ƙi amincewa da ra’ayin cewa hare-haren soja na iya kawo dimokuraɗiyya ko zaman lafiya, yana mai cewa ba za su haifar da ‘yanci ko zaman lafiya ba, sai dai tattaunawa da diflomasiyya mai ɗorewa.

Ya kuma jaddada cewa hanya mafi dacewa ita ce haɓaka zaman tare da fahimtar juna tsakanin al’ummomi ta hanyar tattaunawa.

Sai dai wannan matsayi na Vatican ya bambanta da na gwamnatin Amurka, inda Sakataren yaƙi na ƙasar, Pete Hegseth, ya kare hare-haren.

 

Hakan ya nuna yadda ake samun saɓani mai zurfi tsakanin Vatican da gwamnatocin Washington da Tel Aviv, waɗanda ke ganin hare-haren na da muhimmanci domin tsaron yankin.

Sakon Paparoman ya ja hankalin jama’a a kafafen sada zumunta, inda da dama ke ganin wannan magana tasa gargadi ne kan dogaro da ƙarfin soji wajen warware matsalolin duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!