Labarai
PDP ta yi soka kan sunayen da Tinubu ya tura Majalisa don nada su jakadu

Jam’iyyar adawa ta PDP, ta soki jerin sunayen waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura wa Majalisar Dattawa domin nada su matsayin jakadu, inda ta bayyana jerin sunayen a matsayin abin kunya da kuma takaici.
A cewar jam’iyyar, yawancin waɗanda aka zaba suna laifin da suka shafi rashi gaskiya da almundahana. Daga cikin sunayen da suka jawo ce-ce-ku-ce akwai tsohon Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
PDP ta ce nada shi a wannan lokaci na iya zama ladan zaben da ya bawa shugaban kasa Tinubu nasara, kuma hakan na iya zama barazana ga zaben shekarar 2027.
Jam’iyyar ta bukaci Shugaba Tinubu ya janye jerin gaba ɗaya, ya kuma sake gabatar da mutanen da ke da nagarta, kima, da abin alfahari da za su kare martabar Najeriya a fagen diplomasiyya.
You must be logged in to post a comment Login