Labarai
Jam’iyyar PDP ta yi watsi da umarnin kotu

Jam’iyyar PDP ƙarƙashin shugabancin Kabiru Tanimu Turaki ta yi watsi da hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta bayar wanda ya soke babban taron da ta gudanar a birnin Ibadan na 15 ga watan Nuwamban 2025.
Shugaban jam’iyyar, wanda aka zaɓa a lokacin babban taron na Ibadan, Kabiru Tanimu Turaki ya shaidawa manema labarai a birnin Abuja cewa za su bi matakan shari’a domin ƙwatar haƙƙinsu.
Ya zargi kotun da tafka kuskure a hukuncin da ta bayar, wanda ya fitar da buƙatar da babu wani ɓangare da ya nemi a biya masa, daga cikin masu jayayya da juna.
A ranar Juma’a, 30 ga watan Janairun 2026 wata babbar kotun tarayya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta rusa shugabancin jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki.
You must be logged in to post a comment Login