Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

PDP ta yi korafi kan mai Shari’a Zainab Bulkachuwa

Published

on

Jam’iyyar PDP da dan takararta ta shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar sun shaidawa kotun saurarar korafin zaben shugaban kasa cewa, ‘Da’ ga shugabar kotun daukaka kara Zainab Bulkachuwa, Aliyu Haidar Abubakar, ya ta ya shugaban kasa Muhammadu Buhari yakin neman zabe a yayin zaben shugaban kasa da ya gabata.

A cewar jam’iyyar ta PDP Aliyu Haidar Abubakar ba wai kawai cikakken dan jam’iyyar APC bane ya ma tsaya takarar zaben fidda gwani na gwamnan jihar ta Gombe karkashin jam’iyyar ta APC.

Atiku Abubakar da jam’iyyar sa ta PDP sun ce suna da shafin Aliyu Haidar Abubakar na facebook wanda ke dauke da hotunan sa na kamfen din takarar gwamnan jihar Gombe

Haka zalika a cewar PDP wannan karin hujjoji ne bayan wanda ta gabatar tun da fari na cewa, mijin mai shari’a Zainab Bulkachuwa wato Alhaji Adamu Muhammed Bulkachuwa zabebben sanata ne a mazabar Bauchi ta arewa karkashin jam’iyyar APC.

PDP ta ce bisa ga wadannan hujjoji bai kamata mai shari’a Zainab Bulkachuwa ta jagoranci alkalan da za su saurari korafin zaben shugaban kasa ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!