Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama masu garkuwa da mutane 93

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce, takama masu satar mutane suna garkuwa da su a yankin arewacin Najeriya guda 93.

Mai magana da yawun rundunar DCP Frank Mba ne ya bayyana haka lokacin da ya ke holin batagarin a kauyen Katari da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja.

Ya ce jami’an Operation Puff Adder ne suka samu nasarar kama mutanen cikin makwanni biyu da suka gabata.

A cewar sa, sun samu nasarar kama ‘yan ta’addar ne sakamakon bullo da sabbin dabarun dakile ayyukan batagarin.

DCP Frank Mba ya kuma ce masu satar mutanen suna garkuwa da su an kama su ne a sassa daban-daban na arewa ; kuma an kamasu da bindigogi kirar AK47 guda 35 da AK47 kirar gargajiya guda goma da alburusai guda dari biyar da kuma na’urar harba roka guda daya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!