Labarai
PENGASSAN ta bai wa mambobinta umarnin katse wa matatar Dangote iskar gas

Ƙungiyar manyan ma’aikata a fannin makamashin gas a Najeriya ta PENGASSAN ta bai wa mambobinta umarnin katse wa matatar mai ta Dangote iskar gas nan take.
PENGASSAN ta ce, ta ɗauki matakin ne saboda zargin matatar da korar ma’aikatanta da suka shiga ƙungiyar.
Wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya fitar ta kuma umarci shugabannin rassanta da su katse duk wani bututun mai da ke samar wa matatar ɗanyen man fetur, da ma hana yi wa jiragen ruwa lodi.
Ƙungiyar ta bayyana ɗaukar matakin a matsayin wanda ya zama dole domin kare ‘yancin ma’aikata da tsarin mulki ya ba su na shiga ƙungiya.
A ranar Juma’a ne matatar Dangote ta bayyana korar ma’aikata sama da 1,000, waɗanda ta bayyana a matsayin masu yi mata zagon ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login