Labarai
PENGASSAN ta janye yajin aiki bayan sasantawa da matatar Dangote

Ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya, PENGASSAN ta amince da jingine yajin aikin da shiga bayan samun saɓani da matatar mai ta Dangote
Yajin aikin ne zuwa ne bayan PENGASSAN ta zargi mattaar da korar fiye da ma’aikata 800 saboda sun nuna sha’awar shiga ƙungiyar.
Gwamnatin Najeriya ce ta shiga tsakani a sasancin ɓangarorin biyu da ake yi tun ranar Litinin, to amma sai a yau Laraba ne aka cimma matsaya.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar kwadagon ƙasar ta fitar ta ce matatar ta amince da mayar da ma’aikatan da ta kora domin su ci gaba da aiki da ita.
You must be logged in to post a comment Login