Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

QATAR 2022 QUALIFIERS: Super Eagles za ta karbi rahoto kan lafiyar Samuel Kalu

Published

on

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Gernot Rohr ya ce tawagar likitocin ‘yan wasan kasar nan za su karbi rahoton likitan Samuel Kalu daga Bordeaux.

Rohr ya ce, Super Eagles na bukatar rahoton don sanya ido kan yanayin lafiyar dan wasan yayin da wasanni neman tikitin gasar cin kofin duniya ta 2022 ke karatowa.

Ya kuma ce ya na ci gaba da bibiyar lafiyar Kalu tun da ya dawo bayan da ya fadi a lokacin wasan manyan rukunin kungiyoyin kwallon kafa na kasar Faransa a karshen makon jiya.

A cewar kungiyar likitocin ta Faransa, dan wasan ya sha fama da rashin isasshen ruwa a jikin sa a maimakon matsalolin zuciya kamar yadda aka yi fargaba da farko.

“Likita daga Bordeaux zai aike da dukkan gwaje-gwaje da sakamako ga likitan mu Ibrahim,” in ji Rohr.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!