Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ra’ayoyin Yan Najeriya kan matakin rufe layukan da ba a hada da NIN ba

Published

on

Yan Najeriya da dama ne ke ci gaba da bayyana ra’ayoyin su kan matakin rufe layukan wayar da ba a hada da lambar shaidar katin zama dan kasa ta NIN ba.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki hudu bayan da hukumar sadarwa ta kasa ta fara katse layukan wadanda bas u bi ka’iddojin da ta gindaya ba.

Mafi yawa daga cikin wadanda aka rufewa layukan wayar ta su, na kokawa kan yadda suke gaza samun damar yin kira sai a kira su.

Haka kuma wasun su na ganin cewa matakin ya haifar musu da tsaiko a fannin kasuwancin su.

Musa Abdullahi Kofar Na’isa dan kasuwa ne da ke hada-hada ta Internet ya ce “Tun lokacin da aka fara sanarwar a hade layuka da lambobin NIN na saka, amma kuma kwatsam sai na wayi gari naga layi na yaki kira sai dai a kirani”.

“Yanzu haka bani da damar kiran abokan hulda ta, sai dai in sun kira ni, kuma mafi yawan su bashi suke karbar kayana dukda cewa wasu ban san muhallansu ba” a cewar Musa.

Umar Garba ma ya ce “Ni ban taba samun labarin cewa a hade lamba da NIN ba, ni dai na yi kira a waya naga yaki tafiya naje kamfanin nayi korafi suka fada mun sai na bi wadancan ka’idoji”.

Jamila Isah matashiya ce da ke kasuwancin nau’in kayan abinci ta kafar sadarwar zamani ta ce “Yanzu haka layukana basa tafiya idan na kira mutane bana samu, gashi data ta ta kare nazo zan kara saya na hau whatapp tunda anan nake kasuwanci lamarin ya gagara”.

“Muna bukatar mahukunta da su samar da wani tsari da zai saukaka mana zuwa domin gyara layukanmu, domin mun je kamfanonin da abin ya shafa don yin korafi amma layi yayi yawa” a cewar Jamila.

Zuwa yanzu dai hukumar NCC ta ce, ta rufe layukan waya na sama da mutane miliyan 72 wadanda bas u hade lambarsu da katin dan kasa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!