Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Rahotonni

Rahoto : Gudunmawar makadan gargajiya a kasar Hausa

Published

on

Daga Abdulkadir Haladu Kiyawa :

Makada a kasar Hausa sun bada gudunmawa wajen kwarzanta gwanaye ko kuma kalubalantar wasu ayyuka marasa kyawu a cikin al’umma.

Ka zalika Makadan sun fito da sarakunan gargajiya ta hanyar bayyana halaye dakuma daukakar da suke da ita.

Shin ko matasan wannan zamani sukan saurari irin wadannan wakoki na makadan kasar hauwa?

Shinfida :

Makada da mawakan gargajiya tamkar wani rumbu ne dake dauke da hikima da tarihin al’umma na tsawon lokaci, baya ga haska nasaba da dunkulewar jama’a a matsayin wasu jinsi ko haula ko dangi dake da wata nasaba da juna.

A irin wannan ajiya ne mutane ke ganewa junansu, su kuma iya warware banbanci dake tsakanin wasu kabilu da nasu, da kuma sanya mutane gane abinda iyayensu da kakaninsu sukayi dama kalubalen da suka fuskanta a rayuwa.

Kazalika Makada bawai kawai suna tunatar da al’umma bayansu ne ko jarimtar magabata ba, a’ a, suna tunasar da mutane ko masu mulki cewa kada fa su saki tafarkin iyayensu domin gudun batan tarihi da al’adu.

Ko wacce al’umma ta na da irin nata kidan da wake wake wanda da shi ne suke gina sabuwar alumma da zata wakilci mai shudewa, ganin har yanzu babu wasu kabilu da suka saki kadekadensu na gargajiya domin maye gurbinsu da wasu kade kade don nasu sun gaza.

Dakta Mu’az Mahmud Kudan Shugaban sashen Hausa na tsangayar nazarin harsuna a Jami’ar Sule Lamido ta Jihar Jigawa, ya ce yi wakokin Gargajiya na bada gudunawa a kasar Hausa  sai dai zama ni ya sanya sun koma baya.

Bahaushe dai yace kowa yabar gida-gida yabarshi kana kuma kayan aro baya rufe katara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!