Rahotonni
Rahoto : Yadda mata ke kin sallah akan lokaci sakamakon Kwalliya a Kano
Kwalliya dai wata dabi’a ce mai dogon tarihi a tsakanin mata, inda a zamanin baya mata suke aiwatar da kwalliyar dai- dai da zamaninsu a lokutan bukukuwan aure da sauran hidindimu.
Wakilinmu Abdulbari Ado Sani ya yi nazari kan sauyin zamani da aka samu a bangaren kwalliya a wannan lokaci musamman ma yadda wasu matan ke gaza yin sallah a kan lokaci sakamkon kwalliyar da suka yi.
Ga ƙarin bayani cikin Rahoton Abdulbari Ado Sani :
Da dama daga cikin amare da ma kawayen amaren kan gaza yin salla a kan lokaci ne don gudun bata kwalliyar ta su.
Wannan dai na faruwa ne sakamakon irin yawan kudin da suke kashewa na na yin kwalliyar, inda suke gudun wanje kwalliyar ta su.
Amare da kawayen amaryar dai kan rasa salar azahar da la’asar da magriba da kuma isha’i.
Freedom Radio ta tattauna da wasu ‘yan mata a nan Kano don jin ra’ayoyinsu kan wannan lamari.
“Mu dai muna kwaliyya don birge samarun da kuma nishadi, a wasu lokutan mukan yi idan wata bukata ta taso na biki ko suna”
Malam Umar Sani Fagge babban malamin addinin musulunci a nan Kano, ya yi tsokaci a mahangar addini kan wanan batu.
” Ya kuma bukaci al’ummar musulmi musamman ‘yan mata da iyayensu da su guji duk abinda zai nesanta su da rahamar ubangiji”
You must be logged in to post a comment Login