Addini
Ramadan: Abinda ya sa musulmi suka fi mayar da hankali a goman karshe
Musulmi a goman karshe ta watan azumin Ramadan su kan mayar da hankali wajen yawaita ibada domin samun rabauta da falalar da ta ke cikin kwanakin.
Malamai da dama na kwadaitar da al’umma falalar da ta ke cikin kwanaki goman karshe na Ramadana, musamman yadda suka kasance ana katari da daren Lailatun Kadr daren da ya fi dare dubu.
Nana Aisha R.T.A ta rawaito cewa, idan kwanaki goman karshe na Ramadana yazo Annabi S.A.W na umartar dukkanin iyalansa su tashi su raya daren, kuma suna ninka ayyukan ibada fiye da kowanne lokaci.
Annabi S.A.W ya ce, “A nemi daren lailatul-kadr a kwanakin “MARA” ma’ana daren 21, 23, 25, 27, 29″.
Nana Aisha ta tambayi Annabi S.A.W cewa idan na ga daren lailatul-kadr me zan karanta? Sai Annabi S.A.W ya ce “Ki yawaita karanta Allahu Innaka Afuun Tuhibbul-afwa fa’af’anni”.
Wadannan na cikin dalilan da al’ummar musulmi ke kokarin yin koyi da su wajen kyautata ibadar su da rubanya ayyukan alkhairi da ibada a kwanakin goman karshe na watan azumin Ramadana.
You must be logged in to post a comment Login