Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kaduna zata baiwa daliban sakandire ilimi kyauta

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewar, nan bada jimawa ba zata  aike da kudirin doka ga majalisar dokoki ta jihar don  fafa shirin bada ilimi kyauta kuma tilas ga daliban makarantun sakandire na jihar

Mataimakiyar Gwamnan jihar ta Kaduna Hadiza Balarabe ta bayyana hakan a yayin dake gabatar da kunshin daftarin kasafin kudin badi ga majalisar dokoki ta jihar ta Kaduna wanda ya kai fiye da Naira biliyan dari biyu.

“Daga shekara ta dubu biyu da Ashirin 2020 kowanne dalibin makarantar  na jhar nan zai ci gajiyar karatu kyauta na shekaru goma sha biyu 12’’ A cewar Hadiza Balarabe

Yan bindiga dadi sunyi garkuwa da mutane 8 a jihar Kaduna

Kungiyar Save the children da Action against hunger sun kaddamar da Shirin tallafawa al’umma a jihohin Kano da Kaduna.

Gwamnatin Kaduna za ta daukaka kara kan hukuncin El Zazzaki

Yayin da take bayani kan yadda kasafin kudin zai kasance, Mataimakiyar gwamnan wace ita ce take jan ragamar  gwamnantin jihar ta Kaduna a halin yanzu, ta ce za’a kasha fiye da Naira biliyan dari da casa’in akan manyan ayyuka, yayin d akuma za’a kashe  fiye da Naira.biliyan 67 a ayyukan yau da kullum,tan amai cewar a kulluma gwamnatin jihar na sanya kudorori da manufofin alummar jihar akan gaba fiye da komai.

A dai cikin kunshin daftarin kasafin kudin badi an kebewa bangarorin Ilimi da kiwon lafiya Naira biliyan dari da Arba’in 140, wanda ya kai kasha 73 cikin 100 na kasafin kudin shekara ta 2020.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!