Labarai
Ranar banɗaki: Talauci da ƙaruwar al’umma na haifar da yin bahaya a sarari – Dakta Bashir Getso
Masanin muhalli kuma shugaban kwalejin koyar da harkokin tsafta da lafiya anan Kano ya alakanta talauci da cewa, shi ne ya sanya al’umma ke yin bahaya a sarari sakamakon rashin iya samar da bandaki a muhallan su.
Dakta Bashir Bala Getso ne ya bayyana hakan a wani bangare na bikin ranar banɗaki da ake gudanarwa a kowacce shekara.
Dakta Bashir Bala Getso ya kuma ce, ƙaruwar al’umma da kuma tasirin al’adu a wasu yankunan na taka rawa wajen haifar da matsalar bahaya a sarari.
“Kwararowar baƙi da kuma tasirin al’adun wasu al’ummar na rashin samar da banɗaki a muhallan su, na ɗaya daga cikin dalilan da yake haifar da yin bayaha a sarari musamman a arewacin ƙasar nan”.
“Yawan hayayyafa da ake yi da kuma cinkoson al’umma dukkan su dalilai ne da ke janyo yin bahaya a sarari, kuma barazana ce ga lafiyar al’umma musamman ma ƙanana yara” a cewar Getso.
Dakta Bashir Bala Getso ya kuma ce, haƙƙin shugabanni ne su samar da banɗakuna a wajen hada-hadar jama’a, irin su kasuwanni da tashoshi domin ana iya karɓar baƙi daga sassa daban-daban.
“Yin bahaya a sarari na haifar da cutar kwalara da zazzabin typoid ba ya ga sauran cututtuka da ke saurin yaɗuwa a tsakanin al’umma a wasu lukutan ma suna saurin yin kisa ga ƙananan yara”.
Majalisar ɗinkin duniya ta ware duk ranar 19 ga watan Nuwambar kowacce shekara domin bikin ranar banɗaki ta duniya da nufin magance matsalar yin bahaya a sarari.
You must be logged in to post a comment Login