Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ranar Muhalli: Za mu samar da Dam a ƙaramar hukumar Tofa -Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta fara aikin gina Dam a ƙauyen ƴan Sabo da ke ƙaramar hukumar Tofa.

Ana sa ran kammala aikin samar da Dam din a wannan wata na Yuni don ya tallafa wajen gudanar da Noman Rani.

Kwamishinan muhalli Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyanan haka a wata ganawa da manema labarai a wani ɓangare na bikin ranar muhalli ta duniya da ake gudanarwa a duk ranar 5 ga watan Yunin kowacce shekara.

“Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin da suke da yawan al’umma, a don haka akwai buƙatar kara samar da Dam ƙari akan guda 27 da muke da su” a cewar Getso.

Dakta Kabiru Getso ya kuma ce, ma’aikatar muhalli ta fara aikin shuka bishiyoyi sama da miliyan guda a faɗin jihar domin magance matsalar zaizayar ƙasa da sauran ƙalubalen da muhalli yake fuskanta.

“A bara mun samu nasarar shuka bishiyoyi miliyan ɗaya a faɗin jihar, kuma muna kyautata zaton za su yi tasiri ga muhallan mu, a don haka bana ma za mu shuka guda miliya ɗaya” inji kwamishinan muhalli.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce tuni gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince da dokar kare muhalli, kuma za a ƙaddamar da ita nan ba da daɗewa ba, yayin da dokar hana sare bishiyoyi za a gabatar da ita gaban majalisar dokoki don sahalewa tare da fara aiwatar da ita.

” Babban ci gaban da muka samu a bana shi ne yadda gwamnatin Kano ta yi yarjejeniya da kamfanin sarrafa shara mai zaman kansa na tsawon shekara 20 wanda zai taimaka mana wajen tsaftace magudanan ruwa da sarrafa shara zuwa takin zamani da makamantan su” a cewar Dakta Kabiru Ibrahim Getso.

A ƙudirin gwamnatin na dasa bishiya miliyan ɗaya a bana, kwamishinan muhalli Dr Kabiru Ibrahim Getso ya ƙaddamar da fara dashen shuka a lambun ma’aikatar muhalli duk a wani bangare na bikin ranar muhalli.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!