Labarai
Rashin ƴan Adaidaita ya sanya ana bin dokokin tuƙi – Baffa Babba
Hukumar KAROTA a jihar Kano ta ce, rashin zirga-zirgar babura masu ƙafa a kan titinan Kano ya sanya ana yin tuƙi cikin bin doka.
Shugaban hukumar Baffa Babba Ɗan Agundi ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.
Cikin tattaunawar da aka yi da Baffa ta wayar tarho, wanda ya mayar da hankali kan batun yajin aikin da direbobin adaidaita sahu da suka tsunduma a yau.
“Za ku sha mamakin irin matakin da zai biyo baya sakamakon yajin aikin da suka shiga, domin kuwa za su gane shayi ruwa ne”.
“Mu abinda muka lura da shi ma a yau shi ne, ana gudanar da tuki cikin tsari da doka saboda rashin zirga-zirgar babura masu ƙafa uku, da ma sune ke haifar da jibge tarin jami’an hukumar domin kula da zirga-zirgar ababe hawa a Kano, da babu zirga-zirgar babura masu kafa uku da jihar Kano ta samau sauƙin faruwar wasu haddura da sauran matsalolin tuki”.
A cewar Baffa Babba Ɗan Agundi “Muna jiran umarnin gwamna ne kawai domin mu fara aiwatar da tsarin da doka ta shimfiɗa, don haka duk wanda yaga ba zai yi biyayya ba to yazo ya karɓi kuɗin sa ya ajiye baburin sa domin baya cikin halatattun masu tuƙa babur ɗin a Kano.
Sai dai daga baya Baffa Baffa ya ce, ya karɓi umarni daga wajen gwamna Gandujen kan cewa duk direban adaidaita sahun daya fita aiki a yau, aka lalata baburin sa saboda fitowa da yayi aiki ana yajin aiki da ya garzaya hukumar KAROTA domin a gyara masa.
A safiyar yau Litinin ne dai matuƙa baburan adaidaita sahu suka tsunduma yajin aiki sakamakon batun sauyin lamba da sanin ta takardun tuƙi da hukumar KAROTA ta umarce su da sauyawa.
You must be logged in to post a comment Login