Labarai
Rashin bamu sahihan bayanai a yayin bincike shi ne kalubalen da muke fuskanta – EFCC
Daga Safara’u Tijjani Adam
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta ce babban kalubalen da take fuskanta a nan Kano bai wuce yadda al’umma ke kin ba da sahihan bayanan da take bukata a lokacin da ake gudanar da bincike.
Shugaban hukumar mai kula da shiyyar Kano da Jigawa da kuma Katsina Sanusi Aliyu Muhammad ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freedom Radio.
Ya ce, babu wani shugaba mai rike da madafun iko a nan Kano da yake shiga aikinsu ko kuma ya kawo musu tasgaro wajen gudanar da aikin da suke gudanarwa.
Ya kara da cewa kamata ya yi mutane su daina shiga sabbin tsare-tsaren da ake fito da su na PIN COIN da BEAT COIN, da ke rubanya kudaden da suke zubawa, yana mai cewa wadannan hanyoyin na ‘yan damfara ne.
Sanusi Aliyu Muhammad ya bayyana cewa akwai hukunci da hukumarsu ta ke dauka a kan wadanda suke bayar da bayanan karya a lokacin da suke gudanar da bincike.
You must be logged in to post a comment Login