Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Ba zamu iya yiwa bakin da ke shigowa kasar nan gwajin cutar corona a kyauta ba – PTF

Published

on

Kwamitin kar-ta-kwana na fadar shugaban kasa da ke yaki da cutar corona a kasar nan, ya ce Najeriya ba za ta iya daukar nauyin yi wa dukkannin fasinjojin da ke shigowa kasar nan gwajin cutar Covid-19 kyauta ba.

Babban jami’in kwamitin Dakta Sani Aliyu ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya Mazauna Ketare Abike Dabiri Erewa.

A cewar sa kasar nan ba za ta iya gwajin cutar Covid-19 ga mutane sama da dubu biyar zuwa dubu bakwai a ko wace rana da suke shigowa kasar nan ba.

Dakta Sani Aliyu ya ce a don haka ya zama wajibi fasinjojin su rinka biyan wani kaso na kudi kafin yi musu gwajin cutar ta Covid-19.

 

 

 

AMS/MSH/AMA

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!