Kasuwanci
Rashin kishi ya sanya baƙi ke ƙwace damar ƴan ƙasa a harkar kasuwanci: Gwamnatin Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce son rai da son zuciya ne ya haifar da shigowar baƙi kasar nan don gudanar da kasuwanci da sauran ayyukan yi.
Kwamishinan kasuwanci Alhaji Ibrahim Mukhtar ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio.
Shirin ya mayar da hankali kan batun dokar nan da shugaba Buhari zai yi ta hana baƙi kwararowa ƙasar nan don yin kasuwanci da sauran ayyuka da kan hana ƴan kasar samun dama yi.
Ko da aka tambaye shi anan Kano wacce doka gwamnati ke ƙoƙarin sanyawa kan wannan matsala? Alhaji Ibrahim Mukhtar ya ce, “Ba hurumin gwamnati ba ne sanya doka, domin Gwamnati ba ƴar kasuwa ba ce, illa kawai ta samar da tsare-tsare da dokokin kyautata kasuwanci”.
“Ba matsalar doka ba ce shigowar baƙi kasar nan, illa halayyar ƴan kasuwar ta rashin kishin junan su da kuma rashin bai wa jami’an tsaro goyon baya wajen fitar da baƙi daga ƙasar idan sun shigo”.
Ya ƙara da cewa “Akwai hukumar kula da shige da fice a kasar nan kuma tana da dokoki ga me son shigowa cikin ta tun daga neman tikiti wato “visa” sai ka faɗi abinda zai kawo ka ƙasar ko da kasuwancin ne sai ka faɗi wanne iri kuma zuwa wane lokaci, to amma son rai ya hana abi doka”.
Ya ci gaba da cewa “A nan Kano ne da yawa shagunan kwantin kwari mallakin ƴan China ne amma kuma bahaushe za ka tarar yana yi masa kasuwancin ba tare da kishin kai ba”.
Barista Ibrahim Mukhtar ya ce, hukumar kula da shige da fice ce kaɗai ke da hurumin dakatar da tikitin shigowar kowanne baƙo ƙasar nan matukar ana son kawo ƙarshen matsalar.
You must be logged in to post a comment Login