Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Kasuwanci zai iya shiga wani hali a nan gaba -Mudassir Idris

Published

on

Dan kasuwar nan da ke nan Kano, Alhaji Mudassir Idris Abubakar da aka fi sani da Mudassir and Brothers, ya bayyana fargabar cewa idan har aka cigaba da rayuwar da ake ciki yanzu musamman a bangaren kasuwanci, babu mamaki nan gaba matsalar da za a samu kai cikin mawuyacin hali.

Alhaji Mudassir Abubakar ya bayyana haka ne yau jim kadan bayan kammala shirin ‘Barka da Hantsi’ na nan Freedom Radio.

Ya ce Najeriya za ta iya hana shigo da kaya daga waje, sai dai kuma kamata ya yi gwamnati ta bi hanyoyin da ya kamata ta bi, don tanadar abubuwan da ake bukata, musamman kamfanoni da sauran kayan sarrafawarsu.

Alhaji Mudassir ya kara da cewa kamfaninsa ya yi samu tuntubar wasu bankunan kasuwanci guda biyu da za su baiwa wasu daga cikin abokan huldarsa bashin da ba ruwa don tallafawa jama’a wahalar rayuwar da su ke fuskanta.

Shi ma a tsokacinsa cikin shirin, babban manaja mai kula da harkar kasuwanci ta kafar fasahar sadarwa na kamfanin, Muhammad Zangina Adamu cewa ya yi kafar fasahar sadarwa na taimakawa wajen saukaka kasuwanci musamman ma a lokacin da ake fama da matsalar cutar corona.

Shirin na yau dai ya mayar da hankali ne kan kalubalen da kasuwanci ya samu kansa a ciki da kuma hanyoyin da za a bi don magance matsalar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!