Labarai
Rashin kyautatawa al’umma ne ya janyo rikicin #Endsars – Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce rashin kyautatawa al’umma ne ya janyo rikicin zanga-zangar End Sars a wasu jihohin ƙasar nan.
Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano Kabir Ado Lakwaya ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da rabon tallafi ga matasa.
A cewar sa, tun tuni gwamnatin Kano ta yi nata rabon ga mabuƙata wanda hakan ya taimaka wajen tabbatar da zama lafiya.
Wasu cikin kayayyakin da aka rarraba.
Mai bai wa gwamnan Kano shawara kan matasa Murtala Gwarmai ne ya yi rabon tallafin ga matasa 40.
Murtaka Gwarmai mai bai wa gwamnan Kano shawara kan al’amuran matasa.
Murtaka Gwarmai mai bai wa gwamnan Kano shawara kan al’amuran matasa.
Gwarmai ya ce, ya bayar da wannan tallafin ne domin inganta rayuwar matasa.
A baya-bayan nan dai an samu rikici a wasu jihohin ƙasar nan bayan zanga-zangar neman rushe ƴan sandan SARS.
Wasu cikin kayayyakin da aka rarraba.
Wasu cikin kayayyakin da aka rarraba.
You must be logged in to post a comment Login