Labarai
Rashin mallakar sabuwar manhajar yaɗa labarai zai hana masu kallo ganin tashoshin gwamnati – NBC
Hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa NBC ta ce duk wanda bai mallaki sabuwar akwatun zamani ta Free TV zai Daina kallon tashoshin yaɗa labarai na gwamnati.
Shugaban hukumar Alhaji Balarabe Shehu Illela ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin ƙaddamar da sabuwar manhajar kama tashoshin a gidan gwamnatin jihar Kano.
Illela ya ce, sabuwar manhajar za ta taimakawa ƙasar nan wajen ƙara farfaɗo da tattalin arziƙi.
“Da zarar mun fara amfani da sabuwar manhajar matasa sama da miliyan 1 ne za su samu aikin yi a jihar Kano”.
“Idan manhajar ta fara aiki duk wanda bai mallake ta ba shi da damar kallon tashoshin yada labaran gwamnati, kuma manhajar za ta mayar da hankali wajen yaɗa abubuwan cikin gida fiye da kaso 70 cikin 100”.
Taron ya samu halartar gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero wanda Alhaji Abbas Muhammad Dalhatu ya wakilta da shugabannin gidajen yaɗa labarai na talabijin da Radio da ke faɗin ƙasar nan da ƴan jarida da sauran su.
You must be logged in to post a comment Login