Labarai
Rashin tabbatar da dokar masu bukata ta musamman ce babbar matsalarsu a Kano
Wani wakili na musamman a bangaren masu bukata ta musamman na kungiyar dake wanzar da zaman lafiya ta IPPS ya bayyana cewa ‘har ya zuwa yanzu babbar matsalar masu bukata ta musamman itace rashin basu gurabe na musamman a gwamnatance, duk da doka ta bada damar yin hakan’.
Daya daga cikin masu bukata ta musamman a Kano, Hamza Aminu Fagge ne ya bayyana hakan a Wani bangare na bikin ranar samar da zaman lafiya ta duniya da kungiyar ta hada tare da hadin gwiwar Cibiyar nazarin jinsi na jami’ar bayero a ranar Litinin.
Hamza Aminu Fagge ya ce ‘da majalisa zata tabbatar da dokar, da ya kau da kaso mafi yawan matsalar da masu bukata ta musamman suke fuskanta a cikin al’umna’.
A nata bangaren daraktar Cibiyar nazarin jinsi ta Jami’ar Bayeron Suwaiba Sa’id Ahmad ta ce ‘an shirya taron ne don a raya zaman lafiya a cikin al’umna, tare da shawo matsalar da masu bukata ta musamman ke fuskanta a cikin al’umma’.
Shima daya kasance cikin taron, mai kula da Jin dadi da walwala na Karamar hukumar Nassarawa a ma’aikatan kananan hukumomi na Jihar kano Hassan Abdullahi Garo cewa yayi ‘gwamnati a wannan karon zatayi me yiwuwa wajen ganin ta tabbatar da dokar masu bukata ta musamman, Wanda zai bada damar yi musu ma’aikatan ta musamman, tare da samun mukamai daban-daban a gwamnatance’.
Freedom Radio ta rawaito cewa masu rike da sarauta, da malaman addini, da masana daga jami’o’i daban-daban da masu bukata ta musamman, dama dai-daikun al’umma ne suka halarci taron, da ake fatan za su isar da abinda suka koya a taron ga al’ummar da suke tare, don samarwa masu bukata ta musamman cigaba a cikin a’lumma kamar kowanne ‘dan adam.
You must be logged in to post a comment Login