Labarai
Rashin taimakawa juna ke jawo talauci a Arewa –Kwamrad Dan Mulki
Kungiyar ‘yan asalin jihar Katsina mazauna Kano ta bayyana cewa taimakekeniya da al’ummar Hausawa masu hali ba sa yi ga ‘yan uwan su ga marasa shi a halin yanzu, ke kara karuwar talauci a Arewacin kasar nan.
Shugaban kungiyar, Kwamared Muhammad Ila Dan mulki ne ya bayyana hakan a wajen taron sake zabar sababbin shuwagabannin ta da aka gudanar ranar Asabar a jihar Kano.
Kwamared Ila Dan mulki ya kuma ce irin damarmakin da al’ummar Arewacin kasar nan ke samu a yanzu da su na amfani da su ta hanyar da su ka dace wajen taimakawa ‘yan uwan su masu karamin karfi, da ba za’a tsinci kai a halin da ake ciki na talauci ba.
A jawabinsa lokacin zaben tsohon malami a tsangayar kimiyyar siyasa ta jami’ar Bayero da ke nan Kano, Dakta Aliyu Jibiya, jan hanakalin sababbin shuwagabannin dasu tallafawa ci gaban jihohin Kano da Katsina.
Aliyu Abdurrahman Muhammad, mataimakin shugaban kungiyar ta katsinawa mazauna Kano cewa ya yi, sun shigo kungiyar ne domin taimakawa matasa musamman mazauna Katsina da Kano kan yadda za su rinka gudanar da sana’o’in dogaro dakai domin magance zaman kasha wando.
Shi kuwa a nasa jawabin, Yahaya Usman Danja, cewa ya yi, an kafa kungiyar ne domin samar da hadin kai tsakanin al’ummar ta Katsina ta yadda za su rinka taimakawa junan su ta fannoni da dama.
Yayin zaben, kujeru ashirin da shida ne aka gudanar da zaben a kansu, inda kujeru biyu ne akayi takara a kansu, sakatare da sakataren kudi inda aka zabi Aliyu Garba a matsayin Sakatare, Musa Muhammad Hassan a matsayin Sakataren kudi
You must be logged in to post a comment Login