Labarai
RIFAN: ta bayyana matakan da manoma za su karbi bashi
Kungiyar manoma shinkafa ta Najeriya RIFAN ta ce an samu nasara sosai a noman shinkafar da aka yi a bana duk da cewa an samu matsaloli a sassan da dama a ayyukan noma.
Shugaban kunigyar reshen jihar Kano Alhaji Abubakar Haruna ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan Freedom Radio.
Ya ce abinda kungiyar ta RIFAN ta sanya a gaba shi ne ganin gwamnati ta sakarwa manoma shinkafar wadataccen ruwa domin gudanar da noman rani, da za a iya samun amfani mai yawa.
Alhaji Abubakar Haruna ya kuma ce kungiyar na kokari wajen ganin manoman sun samu bashin da zai tallafa musu wajen bunkasa sana’ar su, yana mai cewa gwamnatin tarayya tana bada bashi ga kowanne manomi ba tare da yin zaben wasu ba.
Ya kuma yi bayanin cewa kamata yayi hukuma ta dukufa ainun wajen ganin an samar da wadattun manoman shinkafa a fadin Najeriya domin ya zamana kasar na iya ciyar da kanta da shinkafar da take samarwa.