Labarai
Rigingimun jam’iyya na mayar da harkokin dimukradiyya baya – Farfesa Kamilu Fagge
Masanin kimiyyar siyasa a jami’ar bayero da ke nan kano, ya ce rigingimun da suke tsakanin jam’iyyu suna haifar da tashe-tashen hankali da kuma mayar da tsarin demokaradiyya baya.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala Shirin barka da Hantsi na nan freedom radio.
Farfesa Kamilu yace samun jam’iyyu da yawa shine zai baiwa mutane damar su zabi abunda suke so saboda dakile rigingimu da Kuma jefe-jefen mugayen kalamai a tsakaninsu.
“Matukar ana so dimukradiyya ta samu ci gaban da ake so, to kuwa sai an samar da wadatattun jam’iyyun da mutane za su zabi wanda suke so karkashin ta” in ji Fagge.
You must be logged in to post a comment Login