Labarai
Rikici ya barke a majalisar dokokin Turkiyya kan batun kasafin badi

Rikici ya barke a zauren majalisar dokokin kasar Turkiyya kan batun kasafin kudin shekarar 2026.
Rahotonni sun bayyana cewa, Dambarwar da faru ne tsakanin ‘yan jam’iyya mai mulki ta AK Party da ‘yan adawa ta CHP, kan Wani bangare na kasafin kuɗin da aka dade ana tafka muhawara a Kai.
Sai dai wannan lamarin ya tilasta wa shugabannin majalisar dakatar da zaman na ɗan lokaci domin shawo kan rikicin.
Koda yake Bayan an dakile rikicin, ‘yan majalisar sun koma zauren domin ci gaba da gudanar da Tattaunawar kafin daga bisani su amince da kasafin kuɗin, kamar yadda tsarin dokar majalisar ta tanada.
You must be logged in to post a comment Login