Ƙetare
Rikici ya sake barkewa tsakanin ƴan tawayen AFC da M23 da kuma dakarun sojin Congo

Rikici ya sake ɓarkewa a gabashin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo tsakanin ƴan tawayen AFC da na M23 da kuma dakarun sojin Congo masu samun goyon bayan ƙungiyar Wazalendo.
Rahotonni sun bayyana cewa, rikicin ya auku ne a wurare da dama a lardunan Arewaci da kudancin Kivu, duk kuwa da rattaba hannu da wadanda ke rikicin da juna suka yi a kan yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin Doha na Qatar.
A arewacin Kivu, an shafe wunin ranar Juma’a ana yin dauki ba dadi, inda hakan ya tilatsa wa mazauna yankin Arcewa daga gidajensu.
Ƙungiyoyin fararen hula na yankin na bayyana damuwa dangane da abin da suke gani a matsayin kudirin ƙungoyoyi masu ɗauke da makamai na karɓe iko da garin Pinga mai matuƙar mahimmanci.


You must be logged in to post a comment Login