Labarai
Rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP ya ƙara yin kamari

Rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP ya ƙara kamari bayan da Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya kai ƙorafi ga hukumar DSS, da kuma babban sifeton yan sanda da kuma hukumar zabe INEC kan zargin sa hannusa na jabu a madadin ofishinsa, cikinn wata wasika da aka aike wa hukumar INEC.
Ya ce bai taɓa sanya hannu a wasiƙar da ke da kwanan wata 25 ga Agusta, 2025 ba, wacce ta shafi shirye-shiryen babban taron jam’iyyar da ake sa ran gudanarwa a Ibadan ranar 15–16 ga Nuwamba, 2025, yana mai neman hukumomi su binciki lamarin.
Wannan rikici ya zo ne yayin da jam’iyyar ke fama da sabani tsakanin magoya bayan Ministan tarayya Abuja, Nyesom Wike, da na Mukaddashin Shugaban jam’iyyar PDP, Umar Iliya Damagum, kan shugabanci da tsarin raba mukamai a yankuna daban-daban.
Matsalolin sun kai har kotu, inda aka samu rikici kan wanda ya cancanci kare jam’iyyar a gaban mai shari’a James Omotosho a Abuja.
A gefe guda, wasu mambobi 14 na kwamitin gudanarwa sun bayyana sunan Chris Uche SAN a matsayin sabon mai ba da shawara na shari’a, bayan sun zargi tsohon lauyan jam’iyya Kamaldeen Ajibade SAN da rashin amana. Sai dai Ajibade ya ƙi amincewa da cirewarsa
You must be logged in to post a comment Login