Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jam’iyyar PDP ta zargi APC da yi wa INEC katsa-landan a zaben Zamfara

Published

on

Jam’iyyar PDP a jihar Kebbi ta ce, kiraye-kirayen ayyana sakamakon zaben gwamnan jihar da jam’iyyar APC ke ba komai ba ne face yin katsa-landan ga hurumin hukumar zabe mai zaman kanta.

Tun bayan da hukumar zabe a jihar ta bayyana sakamakon a matsayin wanda bai kammala ba, wani jigo a jam’iyyar APC Abubakar Garin-Malam, ke ta kiraye-kiraye ga hukumar kan ta ayyana dan takaran APC, Dr. Nasiru Idris a matsayin wanda ya lashe zaben.

To sai dai shugaban kwamitin yada labarai na jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Sani Dododo, a wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin, ya bayyana kiran a matsayin wani yunkuri na raina hukumar zabe ta kasa, INEC.

Alhaji Sani Dododo, ya kuma bukaci INEC da ta yi watsi da kiraye-kirayen na jam’iyyar ta APC tare da yin duk abubuwan da suka dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!