Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Sharhi

Rikicin Femi Fani Kayode da ‘yan jarida a Najeriya

Published

on

Daga Bala Nasir

A makon da ya gabata ma tsohon ministan zirga-zirgar jiragen saman lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo, watau Femi-Fani Kayode ya sake shiga bakin duniya da wata tabargazar, kamar yadda ya saba, inda wannan karon kuma ya yi kakkausan kalamai ga wani dan jarida a fadar gwamnatin jihar Cross river.

Femi-Fani Kayode ya ci zarafin dan jaridar ne saboda tambayar da ya yi masa a kan yadda yake samar da kudin tafiye-tafiyen da yake yi a sassan kasar nan domin gudanar da wani kamfe da har yanzu bai fito sarari ya yi bayani a kai ba.

Dan jaridar wanda ma’aikacin jaridar Daily Trust ne da yake dauko wa jaridar labarai daga jihar ta Cross Rivers ya yi tambayar tasa ne lokacin da shi Femi-Fani Kayode ya gudanar da wani taron ‘yan jarida a gidan gwamnatin jihar a jerin irin wadannan ziyarce-ziyarce da ya ke gudanarwa zuwa jihohi.

Bayan karewa dan jaridar tatas, Femi-Fani Kayode da a yanzu a ke gajarce sunan sa zuwa FFK ya gintse taron ‘yan jaridar da ya kira saboda wai an bashi haushi da tambayar da aka yi masa.

A ganin FFK, tambayar ta kaskantar da shi, sannan kuma cin fuska ce gare shi, a matsayin sa na tsohon minista kuma lauya, wanda ya hada wadannan al’amura guda biyu ya fi karfin a ce bashi da arzikin da zai kai ziyarar jihohin kasar nan gudanar da wani al’amari a karan kansa har sai wani ya bashi kudin yin hakan.

Wannan kuma ya sanya yiwa wancan dan jarida barazana iri-iri bayan zagin da ya yi masa saboda yadda yake kallon matsayin sa a Najeriya, kamar yadda ya nufi wadanda su ke gurin su sani.

Kamar yadda aka sani dai, FFK tun bayan saukar sa daga mukamin minista ya zama mutum ne wanda a iya cewa baya ganin kowa da gashi tare da jin ba wanda ya isa ya taba shi.

A halin da ake ciki dai FFK na gaban kotu bisa tuhumar da a ke yi masa ta tafka almundahana kan aikin sa da kuma laifin cin hanci lokacin ya na minista, har yanzu ba a yanke hukunci ba kan wannan shari’a.

Al’amarin da ya faru a gidan gwamnatin ta jihar Cross River ya bayyana ne ta hanyar hoton bidiyon da a ka dauka na waccan zantawa da ‘yan jaridar, inda aka yada shi a shafukan sada zumunta.

Kafin ka ce wani abu, ‘yan jarida a fadin kasar nan da ma wadanda ke a kasashen ketare su ka yi ta yi masa raddi a kana bin da ya aikata.
Su ma ‘yan kungiyoyi masu zaman kansu sun tari wannan kalubale na tsohon ministan tare da ce masa chas a kulle din da ya cewa ‘yan jarida musamman saboda gudanar da aikin su daidai da ka’idar aiki.

Tabbas! Tambayar da wancan dan jarida ya yiwa FFK a kan turba take, babu wani abu a cikin ta da za a ce ba daidai ba ne, hasali ma irin wannan tambayar ce da ba a yiwa ‘yan siyasa ya sanya su ke ganin kamar su ma’asumai ne, saboda haka suna ganin ba daidai ba ne a yi musu tambaya makamanciyar ta.

Sai dai FFK, bayan ya gano kuskuren sa, sai ya ce, wai ya na neman gafarar abokansa da ma’aikatan jarida, amma wanda ya zaga bai isa komai ba, inda kuma da matsi ya kara yawa, sai ya ce wai yana neman gafarar kamfanin jaridar Daily Trust, wanda ma’aikacin ta ne ya zaga a Calabar, daga bisani ya dawo ya baiwa dan jaridar da ya zaga hakuri.

Wannan ya nuna cewa kenan duk wanda ka ga ya gagara to kyale shi a ka yi, amma abin takaici a nan shine yadda har zuwa wannan lokaci wasu daga cikin shugabanni a wannan yanki na Arewa suke shakkar FFK.

Saboda irin fandarewar FFK, duk wannan ba ta hana shi daukar matakin ta-nutsu ba, tare da jin kunyar laifin da ake tuhumarsa da shi a matsayinsa na wanda aka dorawa nauyin tafiyar da al’amuran jama’ar kasa.

Watakila rashin ta-ido da FFK, ke ji da shi ne ya sanya wasu daga cikin manyan mu da ke nan Arewa ke shakkarsa, wanda hakan ya sanya suke lallabarsa domin ya sassauta musu ko kuma ya yabe su.

Babu wanda FFK ya raina a duniyar Najeriya sama da mutanen wannan yanki namu na Arewa, a Arewar kuma ba wanda ya fi renawa sama da al’umar Hausawa da Fulani, amma duk da wannan a ka dauki sarauta aka ba shi a jihar Zamfara.

Mutane da yawa sun nuna rashin amincewar su da wannan lamari, inda har wasu matasan yankin suka fito suka yi ta balokoko kan hakan, amma duk wannan, ba wanda ya saurare su ballantana ma ya sake lale.

Ya zuwa yanzu dai reshen kungiyar ‘yan jarida ta kasa, NUJ na jihohi biyu sun hana mambobinsu daukar rahoton duk wani lamari da FFK din ya shirya.

A gaskiya wannan kokari ne da ya kamata ai yabawa, saboda daukar irin wadannan matakai ne zai sanya wasu mutane da ke ganin ‘yan jarida ba a bakin komai suke ba, su sake tunanin.

Rashin daukar mataki kan duk mahalukin da ya wulakanta ‘yan jarida ne dama ke sanyawa a na yi musu wulakancin tare da kaskanta su a wurare da dama.
Lokaci ya yi da kungiyar NUJ za ta koma daki ta sake duba irin halin rayuwar aiki da ‘ya’yan ta suke fuskanta tare da yin nazari sosai domin fito da matakan da suka dace domin dawo da martabar aikin da kuma na ‘ya’yanta.

Ba wanda zai gyara maka dakin da kake kwana a ciki domin kuwa bai san halin da kake ciki ba a cikin sa, wajibi ne lamarin FFK ya zame izinar daukar matakin gyaran kungiyar ga shugabanni da dukkan masu ruwa-da-tsaki a aikin jarida a kasar nan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!