Kowane Gauta
Rikicin siyasa na kara ruruwa a kasuwar Kantin Kwari
Bilal Musa Bakin Ruwa jami’in hulda da jama’a na Kungiyar Kima ta kasuwar kantin kwari ya kalubalanci gwamnatin jihar Kano kan gaza gudanar da zabe a kasuwar.
Yana mai cewar rashin gudanar da zabe a Kasuwar ta Kantin Kwari ya sanya ake tafka kura-kurai.
Bilal Musa ya shaida hakan ne ta cikin shirin Kowane Gauta na gidan Radio Freedom.
Yana mai cewa shekara da shekaru gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kasa gudanar da zabe a kasuwar wanda yasa yanzu kowane kamfani ke yin abinda ya ga dama a kasuwar.
Bilal ya kara da cewa babu wata rawa da shugabancin ruko na kasuwar ke gudanarwa a yanzu haka , domin kawo gyara musamman akan kamfanoni dake yin badai-dai-ba ko cin-karen-su-ba-babbaka a kasuwar wanda ya sabawa doka amma sun kasa takubaka komai akai.
Yace mafita kawai gwamna Ganduje ya fitar da tsarin gudanar da zabe a kasuwar domin hakan shine kadai zai fi a’ala a kasuwar baki daya.
Su dai ‘yan kasuwa da dama na kukan rashin ciniki a halin yanzu kasancewar al’umma na cikin wani hali tun bayan da kasar nan ta shiga cikin jerin kasashen da fuskanci annubar Corona.
You must be logged in to post a comment Login