Connect with us

Labarai

Siyasa : Yadda kotun koli ta tabbatarwa Yahaya Bello nasarar sa

Published

on

Kotun kolin kasar nan ta tabbatar da nasarar da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya samu a zaben da aka gudanar ranar 16 ga watan Nuwamban bara.

Kotun kolin dai ta yanke wannan hukunci ne a yau Litinin bayan da daukacin alkalan kotun suka amince da hukunci.

Alkalan da suka yanke hukuncin sun hadar da alkalin alkalan kasar nan Mai shari’a Tanko Muhammad da mai shari’a Olabode Rhodes-Vivour sai Sylvesta Ngwuta da mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun da mai shari’a Inyang Okoro da Amina Augie da kuma mai shari’a Uwani Abba-Aji.

Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben na bara Musa Wada wada ne dai ya daukaka kara zuwa kotun yana kalubalantar zaben da cewa, an gudabar da shi ne cike da kura-kurai tare da magudi da kuma arigizon kuri’u.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Archives