Manyan Labarai
Siyasa: Shin ritayar da Ganduje yayiwa Kwankwaso ta tabbata?
Jim kadan bayan kotun koli ta tabbatar da nasarar da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a zaben shekarar bara wasu daga cikin magoya bayan Gwamna Ganduje suka rika kai ziyarar taya murna ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A irin jawaban da gwamnan ya rika yi an rawaito cewa Gwamnan ya ayyana ritayar siyasa da yayiwa tsohon amininsa a siyasance kuma tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.
Hakan ya biyo bayan tataburza da gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi kafin ya koma mukamin nasa na gwamnan Kano.
Masu bibiyar al’amuran yau da kullum sun san cewar Gwamnan jihar Kano mai ci a yanzu Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sha tataburza kafin ya lashe zaben gwamna a watan Maris na shekarar ta bara.
Sai da ta kai an kai zagaye na biyu kafin a bayyana wanda ya lashe zaben gwamnan na jihar Kano.
Bayan rantsar da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne babban abokin karawarsa a zaben gwamnan na Kano kuma dantakarar jamiyyar PDP Injiniya Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara a gaban kotun sauraran kararrakin zaben gwamna yana kalubalantar ayyana gwamna Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.
Kotun sauraran kararrakin zaben wanda mai shariah Halima Shamaki ke jagoranta ta yanke hukunci da cewa gwamna Abdullahi Ganduje ne ya lashe zaben na gwamnan Kano.
Sai da ta kai Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kai ga kotun kolin kasar nan domin ganin ya tabbatar da an yanke hukunci, sai dai duk hukunce hukunce da kotun kasa da na kolin suka yi babu wacce ta bawa Abba Kabir nasara.
Duk da cewa ba tsohon aminin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsaya takarar gwamna ba wato injiniya Rabiu Musa Kwankwaso sai gashi gwamna Ganduje na cewa yayiwa Kwankwaso ritaya a siyasar Najeriya.
Amma ana ganin dalilan da yasa gwamna Ganduje yace yayiwa Kwankwaso ritaya a siyasar Najeriya hakan ba zai rasa nasaba da cewa dantakarar gwamna na jamiyyar PDP Abba Kabir Yusuf jagoran jamiyyar PDP kuma tsohon Gwamna Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ne ya tsayar da shi.
Buhari ya nada Abdulrahman Baffa Yola a matsayin mai takaimakasa a harkokin siyasa
Shugaba Buhari yayi ganawar sirri da wasu tawagar yan siyasa daga Kano
Masharhanta al’amuran siyasa na ganin cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai dauki abokin takarar sa lokacin zaben gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin barzana gare shi a siyasa ba, illa tsohon amininsa kuma tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.
Hakan ba zai rasa alaka da raba gari da suka yi a siyasa ba tun bayan shi tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya tsayar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda zai gaje shi a zaben shekarar 2015.
Bayan gwamna Ganduje ya lashe zaben ne ,rigimar siyasa ta kunno kai a jihar ta Kano inda Gwamna Ganduje ya bar gidan siyasar Kwankwasiyya shima ya kafa gidansa wanda ake kira da Gandujiyya.
Shima tsohon gwamna Inijiniya Rabiu Musa Kwankwaso an taba rawaitowa cewa ya taba yin ikirarin zai yiwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da shugaban kasa Muhammadu Buhari ritaya a siyasa.
Amma Gwamna Ganduje bai mayar da martani ba sai bayan fiye da shekara daya da ikirarin da aka ce tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso yayi na yiwa Gwamna Ganduje da shugaba Muhammadu Buhari ritaya a siyasar Najeriya.
Ko shin menene yin ritaya a siyasa kamar yadda ‘’yan siyasar biyu suka rika ambatawa,wato Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso?
Idan har ritaya a siyasa shine faduwa zabe ko rasa mukami na siyasa to shi kansa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya taba yi musu ritaya a siyasa a shekarar 2003 har zuwa shekarar 2011.
Ko hukuncin Kotun Koli ya kawo karshen Siyasar Kwankwasiya a Kano?
Ko babban Akanta na Najeriya zai yi takarar Gwamnan Kano?
A tsawon shekaru takwas da Malam Ibrahim shekarau yayi yana mulkin Kano sai da aka daina jin duriyar tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso musamman ma tsohon mataimakinsa Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Duk da gwamnatin tarayya zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta bawa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ministan tsaro shi kuma Dr Abdullahi Umar Ganduje ya zama mai taimaka masa na musamman yanayin siyasar Kano sai da ya juya musu baya.
Har sai a shekarar 2011 da suka sake lashe zabe a karkashin jam’iyyar PDP sannan yanayin siyasar Najeriya ya fara yi da su har zuwa yanzu.
Ko yaya wannan ritaya da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace yayi wa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso zata kasance ?