Connect with us

Labaran Kano

Rotary ta bawa hukumar KAROTA tallafin kayan bada hannu

Published

on

Daga Shamsu Dau Abdullahi

Kungiyar Rotary Club ta kaiwa  hukumar Karota ziyara domin nuna mahimmanci da hukumar take bayarwa na tsaftace ka’idojin hanya.

Shugaban kungiyar Rotary Bidemi Nuradden yace sun kawo tallafin ne domin nunawa sauran kungiyoyi su rika tallafawa hukumomin tsaro da kayan aiki na bada hannu.

Ya kara da cewa wannan abun yana da mahimmanci a wajen bada hannu a kan titi musamman ma  titunan da ‘’yan makaranta suke tsallakawa zuwa gida da makaranta.

Hukumar Hisbah ta Kano ta cimma yarjejeniyar aiki da KAROTA

Kano: Hukumar KAROTA ta kai sumame wajen boye magunguna

Shugaban hukumar ta Karota Baffa Babba Dan Agundi yace suna son kungiyoyi su rika taimakawa hukumomin tsaro domin ta hakane za’a samu cigaba a jihar Kano.

Nan take hukumar ta Karota   ta fara raba kayan da kungiyar ta kawo hukumar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,999 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!