Labaran Kano
Rufe Boda: Wasu kamfanunuwa sun samu koma baya
Sakamakon rufe boda da gwamnatin tarayya tayi a shekarar bara wasu kamafanoni suna samun koma baya wajen fitar da kayayyakin da suke samarwa.
Shugaban kungiyar masu masana’antu na yankin rukunin masana’antu na Bompai Sani Husseini Sale ne ya bayyana haka a cikin shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio.
Sani Hussieni Sale ya kara da cewa bayan kaji da kayan noma da suke samun tagomashi sakamakon rufe boda har yanzu da sake a wasu kayayyakin da masana’antun Najeriya ke fitar wa.
Hukumar EFCC ta cafke masu kamfanin boge da bindigu a Kano
Ana zargin hukumar kasuwar Kantin Kwari da zama saniyar tatsa – Anti Kwarrafshan
Sani Husseini Sale ya kara da cewa kayayyaki kamar tabarma da robobi da masana’antun jihar Kano suke samarwa zuwa kasashen Chadi da Nijar da Sudan da Kamaru basa samun fitar da kaya sakamakon rufe boda.
A nasa bangaren wani dankasuwa daga bangaren kasuwar Singa Ambasada Garba mai Maggi ya bayyana cewa yace bayan alfanu da rufe boda akwai kuma matsaloli da rufe bodar ke tattare da shi kamar tarnaki ga ‘’yan kasuwa.