Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Rufe Boda: Wasu kamfanunuwa sun samu koma baya

Published

on

Sakamakon rufe boda da gwamnatin tarayya tayi a shekarar bara wasu kamafanoni suna samun koma baya wajen fitar da kayayyakin da suke samarwa.

Shugaban kungiyar masu masana’antu na yankin rukunin masana’antu na Bompai Sani Husseini Sale ne ya bayyana haka a cikin shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio.

shugabannin MAN da na yan Kasuwa

Sani Hussieni Sale ya kara da cewa bayan kaji da kayan noma da suke samun tagomashi sakamakon rufe boda har yanzu da sake a wasu kayayyakin da masana’antun Najeriya ke fitar wa.

Hukumar EFCC ta cafke masu kamfanin boge da bindigu a Kano

Ana zargin hukumar kasuwar Kantin Kwari da zama saniyar tatsa – Anti Kwarrafshan

Sani Husseini Sale ya kara da cewa kayayyaki kamar tabarma da robobi da masana’antun jihar Kano suke samarwa zuwa kasashen Chadi da Nijar da Sudan da Kamaru basa samun fitar da kaya sakamakon rufe boda.

A nasa bangaren wani dankasuwa daga bangaren kasuwar  Singa Ambasada Garba mai Maggi ya bayyana cewa yace bayan alfanu da rufe boda akwai kuma matsaloli da rufe bodar ke tattare da shi kamar tarnaki ga ‘’yan kasuwa.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!