Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta kama masu laifi sama da dubu 1

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta kama sama da mutane 1, 700 da suka aikata laifu daban-daban.

Kwamishinan ƴan sandan na jihar Aliyu Adamu ne ya bayyana hakan, a wani ɓangare na bankwana da rundunar sakamakon sauyin wajen aiki da ya samu.

Ya ce, rundunar ta kama sama da mutane 1,700 da suka aikata laifin garkuwa da mutane , fyaɗe, fashi da makami, masu Safarar miyagun ƙwayoyi da sauran su.

Cikin abubuwan da rundunar ta ƙwato sun haɗa da bindiga ƙirar AK47 guda 20 sai tarin ƙwayoyin maye irin su tabar Wiwi da sauran su.

Aliyu Adamu ya ce, tuni an gurfanar da su a gaban kotu don yanke musu hukunci daidai da abinda suka aikata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!