Labarai
Rundunar ƴan sandan Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 5 sakamakon fashewar wani abu

Mummunar fashewar wani abu ya faru a wani kamfani da ke Eastern Bypass a jihar Kano, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 5 tare da jikkata wasu 10.
Lamarin dai ya faru ne da safiyar yau Asabar, inda wani abu da ake kyautata zaton Bam da ake zargin ya na cikin wata babbar mota ya tarwatse.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
A cewarsa, motar da lamarin ya shafa ta fito ne daga jihar Yobe, ba tare da wani cikakken bayani ba.
Kwamishinan ƴan sandan ya ƙara da cewa har yanzu hukumomi ba su tabbatar da ainihin musabbabin fashewar ba, ko kuma mallakar abubuwan fashewar ba.
An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano AKTH, inda aka tabbatar da mutuwar mutane biyar, kuma 10 na samun kulawa.
Kwamishinan bai cewa tabbatar da ko akwai ma’aikata a cikin waɗanda abun ya shafa ba, yana mai cewa binciken zai bayyana wasu bayanai game da lamarin.
CP Bakori ya bayar da tabbacin cewa ƴan sanda za su gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin fashewar.
You must be logged in to post a comment Login