Labarai
Rundunar Ƴan sandan jihar Kano ta haramta yin hawan Sallah

Rundunar Yan sandan jihar Kano ta haramta yin hawan Sallah a duka fadin jihar domin samar da tsaro a fadin jihar sakamakon rahotanni da hukumar ta samu domin bayar da tsaro a kano
Kwamishinan yan sandan jihar Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Manema labarai a yau juma’a cikin shirye shiryen bikin sallah ƙarama
Ya kuma ce hakan na zuwa ne biyo bayan tattaunawa da sukai da hadakar jami’an tsaro kan matsalolin rashin tsaron da za a iya samu idan aka bari aka gudanar da hawan.
Kwamishinan yan sandan ya kuma ce duk wanda aka samu da gudanar da kilisa a lokutan bikin sallah to ya zama wajibi doka ta yi aiki akan sa domin samar da tsaro a fadin jihar kano
You must be logged in to post a comment Login