Tsaro
Rundunar yan sandan Kano ta shirya yin gwajin kayan aikin tsaro
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce, da misalin karfe 12:00 na ranar gobe Lahadi za ta gudanar da wani Atisayen nuna karfin kayayyakin aikin kwantar da tarzoma da rundunar ke da su domin a jiye su a guraren da aka tsara.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Muhammad Hussain Gumel, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai da yammacin yau Asabar.
Muhammad Gumel ya ce, ba wai suna so su tsorata mutane ba ne yayin Atisayen da zasu gudanar, kawai dai za su yi hakan ne domin ya zama gargadi da jankunne ga masu kokarin tayar da fitina a Kano.
A cewarsa babu wani mahaluki da rundunar ‘yan sandan Kano za ta saurara wa matukar ya yi yunkurin tayar da husuma a zabe ko kuma bayan fitar da sakamako.
You must be logged in to post a comment Login