Connect with us

Labarai

Rundunar yan sanda ta tabbatar da mutuwar jami’anta bakwai

Published

on

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya ta tabbatar da mutuwar wasu jami’an ta bakwai, sakamakon harin wasu ‘yan bindiga da ya rutsa da su yau a marabar Galadimawa da ke Abuja.

Kwamishin rundunar ‘yan sandan a Abuja Sadiq Bello ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai, inda yace ‘yan bindigar sun fadawa jami’an yan sandan ne da tsakar ranar yau a lokacin da suke gudanar da aikin sintiri a yankin na Galadimawa.

Rahotanni sun bayyana cewa Kwamishinan ‘yan sandan be yi cikakken bayani game da faruwar al’amarin ba, sai dai yace kakakin rundunar Anjuguri Manzah zai fitar da sanarwar cikakken bayanai game da al’amarin.

Kisan jami’an ‘yan sandan na zuwa ne kwanaki uku kenan da kisan wasu jami’an ‘yan sanda a jihar Akwa Ibom da biyo bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai musu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Akwa Ibom Odiko MacDon ya tabbatar da mutuwar jami’an biyu, tare da cewa yanzu haka sun fara gudanar da bincike kan wannan al’amari

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!