Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar sojan Najeriya da ta kasar Kamaru sun ce sun kashe mayakan Boko haram 35

Published

on

Rundunar sojin kasar nan da takwararta ta kasar Kamaru sun ce sun kashe mayakan Boko-Haram guda talatin da biyar.

 

Haka kuma sojojin kasashen biyu sun ceto wasu mutane dari shida da uku wadanda Boko-Haram su ka yi garkuwa da su.

 

Mataimakin daraktan yada labarai na rundunar Operation Lafiya Dole Kanal Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka ga manema labarai, yana mai cewar wannan wani bangare ne na kammala fatattakar ‘yan boko-haram daga arewa maso gabas.

 

A cewar sa sojojin sun kai farmaki ne a yankunan Kusha-Kucha da Surdewala da Alkanerik da Magdewerner da kuma kauyen Mayen dukkannin su da ke kan iyakar kasar nan da Kamaru.

 

Haka kuma a cewar sa sojojin sun samu nasarar lalata makamai guda goma sha biyar da bama-bamai da babura da kuma kekunan

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,434 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!