Labarai
Rundunar sojan Najeriya ta harbe yan bindiga 78 a watan jiya
Dakarun Sojin Najeriya na rundunar Operaion Hadarin Daji sun sanar da cewa sun samu nasarar harbe ‘yan bindiga 78 tsakanin watan jiya zuwa na Yulin nan da mu ke ciki.
Haka kuma rundunar ta ceto mutane 50 da aka yi garkuwa da su sannan suka kwato bindigogi 47 kirar AK47 da bindiga 1 mai sarrafa kanta, sai bindigogin garkajiya guda 14 da kanana kirar Pistol guda, da kuma tarin harsasai kusan 2,500.
Mai rikon mukamin draktan yada labarai na shelkwatar tsaron kasar nan Kanar Onyema Nwachukwu ne ya sanar da hakan jiya talata a Abuja yayin ganawa da manema labarai, yana mai Karin hasken cewa sun gano shanu 2,278 da kuma Babura 14.
Ya ce rundunar Sojin ta Operation Hadarin Daji wadda aka kafa don yaki da matsalolin tsaron da suka addabi arewacin Najaeriya, za ta ci gaba da farautar ‘yan bindigar a duk inda su ke, sannan a gurfanar da su gaban Kotu da zarar an kammala bincike.
Haka zalika ya yi tsokaci kan rundunar Operation Thunder Strike da aka kaddamar don yaki da masu sacewa da kuma garkuwa da mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda ya ce sun kashe ‘yan bindiga 6 sannan suka kama 14 a wurin.
Kanar Nwachukwu ya kara da cewa sun gano maboyar ‘yan bindigar a garuruwan Jere da Katare da Rijana da kurmi-Karshi, sai Gidan-Mamman Black Gold da kuma Gidan-Guza.