Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar Sojan sama na Atisaye a Kano

Published

on

Shugaban rundunar Sojojin sama ta kasa Air Vice Marshall, Abubakar Saddique , ya ce rundunar zata cigaba da bada kariya ga dukkanin filayen jiragen sama da al’ummar kasar nan tare da inganta harkokin tsaro a dukkanin wajen da ya kamata.

Air Vice Marshall Abubakar Siddique , ya bayyana haka ne a jiya a filin jirgin saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano, a bikin motsa jiki da faretin nuna karfin Soji, mai taken “Exercise Steel Dome 2” da aka gudanar.

AVM Saddique, yace  hakika sanin kowa ne kasar nan na fama da kalubalen  tsaro daban-daban, don haka yasa rundunar sojin sama ta shirya irin wannan tare da fito da sabbin hanyoyin zakulo kare filayen jiragen saman kasar nan da ga ‘yan ta’adda a bangare daya kuma ta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar kasar nan.

Batutuwa masu nasaba

Rundunar Sojan Najeriya ta bukaci al’umma da kar su tsorata sakamakon harbin Bindiga ranar Talata

Farfelar jirgin saman rundanar sojin kasar nan ya fille kan want hafsan sojin sama

Rundunar sojan Nijeriya ta ce ta cafke wani mai hada bama-bamai kungiyar Boko Haram

Rundunar sojan kasar nan ta sanar da hallaka yan bindiga dadin 35

Da yake nashi jawabin gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya kasance Babban bako a wajen taron, yace gwamnatinsa a shirye take ta hada kai da dukkanin jami’an tsaro don ganin an samar da tsaro da zaman lafiya , tare da jaddada kudirin gwamnatin sa na yin taron masu ruwa da tsaki kowanne wata don lalubo bakin zaren samar da zaman lafiya mai dorewa.

Wakilinmu na fadar gwamnatin jiha Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa , an gudanar da faretin girmamawa da nuna karfin Soji da kuma dabaru na kariya a matakan gaggawa wanda manyan ofisoshin  rundunar sojin sama dake nan Kano suka jagoranta a safiyar yau.

 

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!