Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar sojan Nijeriya ta ce ta cafke wani mai hada bama-bamai kungiyar Boko Haram

Published

on

Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta sun cafke wani mutum daya shahara wajen hada bama-bamai ga mayakan kungiyar Boko Haram.

 

Rundunar ta ce an cafke Adamu Hassan ne da ake yiwa lakabi da suna ‘baale’ a garin Kaltungo na jihar Gombe.

 

Mai magana da yawun rundunar Operation Lafiya Dole Kanar Onyema Nwachukwu, ya ce an cafke mutumin ne a wani samame da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya suka kai a jiya.

 

Rahotannin sun  ambato Kanar Nwachukwu na cewa dakarun sojin kasar nan sun kashe mayakan Boko Haram uku a bata kashi da suka yi a tsaunukan Bokko Hilde da ke kan hanyar Ngoshe zuwa Pulka a jihar Borno.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!