Connect with us

Labarai

Rundunar  Sojin ƙasar nan ta cafke wani mai safarar makamai

Published

on

Rundunar  Sojin ƙasar nan dake aiki karkashin  Runduna ta 6 sun cafke wani da ake zargi da safarar makamai tare da kwato harsasai 969 a Sarkin Kudu da ke Karamar Hukumar Ibi ta Jihar Taraba.

 

Hakan  na cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaran Runduna ta 6, Laftanar Umar Muhammad, ya fitar aka rabawa manema labarai.

 

Sanarwar ta ce an cafke Monday Reuben mai shekaru 48 dan Karamar Hukumar Numan ta Jihar Adamawa, a wani shingen bincike bayan samun sahihin bayanan sirri.

 

Rundunar ta kwato bindigogi kirar AK 47 akwati guda  mai dauke da harsasai 250, fakiti 14  mai dauke da harsasai 700, da harsasai 19,  da kudi Naira miliyan 2,440,000, tare da wasu kayayyaki.

 

Sanarwar ta kara da cewa ana tsare da wanda ake zargin tare da kayayyakin da aka kwato domin mika su ga hukumomin da suka dace don ci gaba da bincike.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!