Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji sun hallaka yan bindiga guda biyar, a Kaduna

Published

on

Dakarun sojin Nijeriya na runduna ta daya da ke aiki a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga guda biyar, tare da kwato bindigogi kirar AK47 guda hudu.

Mai rikon mukamin mataimakin daraktan yada labaran rundunar Laftanar Kanar Musa Yahaya ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Juma’a.

Kanar Musa Yahaya ya ce wannan wani bangare ne na aikin fatattakar ‘yan bindigar da suka addabi yankin arewa maso yammacin kasar nan.

Inda suka kai samame wurare irin su titin Kanti zuwa Tantatu da ke Dajin Kubusu, da kuma yankin Tuddan Kaso a jihar ta Kaduna.

Sanarwar ta ce sauran makaman da aka gano a hannun ‘yan bindigar sun hada tarin harsasai da Babura guda uku da adda guda daya da wayoyin hannu guda biyu da kuma kayan tsubbace-tsubbace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!