Labarai
Rundunar sojin kasar nan ta kashe akalla mayakan ISWAP 11 a jihohin Borno da Adamawa

Rundunar sojin kasar nan ta ce ta kashe akalla mayakan ISWAP goma sha daya a farmakin da ta kai jihohin Borno da Adamawa.
Cikin wata sanarwa da rundunar hadin gwiwa da ke yaki da mayakan Boko Haram da ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar ta fitar a ranar Talata, ta ce ta yi nasarar kashe mayakan na ISWAP a wani artabu a hanyar Baga da ke jihar Borno da kuma yankin Madagali a jihar Adamawa.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin bayan da mayakan Iswap suka yi wa dakarun sojin kwanton bauna a kusa da Garin Giwa a karamar hukumar Kukawa, inda suka dasa bom tare da bude wuta.
Sai dai sanarwar ta ce sojojin sun yi nasarar murkushe harin tare da kashe mayakan ISWAP takwas ciki har da kwamandojin kungiyar biyu, kuma sojojin sun yi nasarar kwato makamai da Babura.
Haka kuma rundunar sojin ta ce dakarunta tare da taimakon mafarauta da yan sakai sun kashe wasu karin mayakan uku tare da karbe makamansu a jihar Adamawa.
You must be logged in to post a comment Login