Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Takaitaccen tarihin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II

Published

on

An haifi Sarkin Kano na goma sha hudu a daular Fulani Malam Muhammadu Sanusi na biyu a ranar talatin da daya ga watan Yulin alif da dari tara da sittin da daya (1961) anan Kano.

Kuma ya fito ne daga cikin zuri’ar sarki Dabo.

Mahifinsa Aminu Sanusi fitaccen ma’aikacin diflomasiya ne wanda ya yi aiki a kasashen Belgium, China, da kuma Canada sannan daga bisani ya zama babban sakatare a ma’aikatar kasashen wajen kasar nan.

A bangare guda an kuma nada shi a matsayin Chiroman Kano kuma ‘Da’ ne ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na daya wanda ya mulki Kano tsakanin 1953 zuwa 1963 kafin murabus din sa.

Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya fara karatun Islamiyya a gaban mahaifinsa, inda ya yi saukar Al-Kur’ani da kuma hadisan ma’aiki, Bugu da kari ya kuma halarci makarantar firamare ta Saint Annes da ke unguwar Kakuri a Kaduna, yayin da a 1973 ne Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya shiga kwalejin King’s College da ke Lagos, inda ya kammala a 1977.

Sarki Muhammadu Sanusi na biyu ya kuma halarci jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari’a a jihar Kaduna, inda ya kammala Digiri akan nazarin tattalin arziki a 1981.

Bayan kammala jami’a ya gudanar da hidimar kasa a tsohuwar jihar Gongola wato jihar Adamawa da Taraba a yanzu, inda ya koyar a wata makarantar mata ta kwana a Yola babban birnin jihar Adamawa.

Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya sake komawa jami’a, inda ya samu digiri na biyu a nazarin tattalin arziki, kafin daga bisani ya koyar a jami’ar ta Ahmadu Bello har ta tsawon shekaru biyu.

Sarkin Kano na goma sha hudu a daular Fulani ya kuma halarci jami’ar Internatiuonal da ke birnin Khartoum a kasar Sudan a 1997, inda ya samu digiri akan shari’a da addinin Islama.

A jami’ar ta Khartoum Sarkin na Kano ya mai da hankali ne wajen nazarce-nazarcen ayyukan fitattun masana falsafa na musulunci da na yammacin duniya irinsu: Plato, Aristotle, Al-Ghazali, Ibn Rushd, Ibn Taymiyyah, Ibn Khaldun da sauransu.

A bangare guda masani ne kan mahzobobi na ahlil sunna da suka hada da: Hanafi, Maliki, Shafi’I da kuma Hanbali.

A 1985 ne ya fara aikin banki bayan da aka dauke shi aiki, a Icon Limited wanda wani bangare ne na Barings Bank and Morgan Guaranty Trust, inda ya kasance babban jami’in da ke kula da harkokin kudi a shiyyar bankin da ke nan Kano.

A 1991 ya bar bankin bayan da ya tafi kasar sudan karatu.

Haka kuma a 1997 ya dawo gida Nigeria, inda ya fara aiki da bankin UBA, inda ya kai har janaral manaja a bankin kafin daga bisani a shekarar 2005 ya zama mamban gudanarwa na bankin sannan babban darakta mai kula da tsimi da kudi. A shekarar 2009 aka nada shi a matsayin shugaban bankin First bank kuma dan arewa na farko da ya taba rike wannan mukamin.

Haka zalika a ranar daya ga watan Yuni ne aka bayyana sunansa a matsayin sabon gwamnan babban bankin kasa CBN a lokacin mulkin shugaba Umaru Musa Yar’adua, inda a ranar 3 ga watan Yuni ne a shekarar ta 2009 majalisar dattijai ta amince da shi.

A ranar 8 ga watan Yuni a shekarar 2014 ne gwamnatin Kano ta nada Malam Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin sabon Sarkin Kano na goma sha hudu a daular Fulani bayan rasuwar Sarkin Kano na lokacin, Alhaji Ado Abdullahi Bayero a ranar 6 ga watan Yuni a shekarar ta 2014.

An kuma sauke shi daga karagar mulki a ranar 9 ga watan Maris a shekarar 2020.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!